Maryam Sanda ta daukaka Kara kan hukuncin kisa
Friday, February 21, 2020
Add Comment
Maryam Sanda ta daukaka kara a babbar Kotun Daukaka Kara da ke Abuja don kalubalantar hukuncin da aka yanke mata na kisa, sakamakon samun ta da laifi da babbar kotu ta yi na kashe mijinta.
A watan Nuwamban 2017 aka zarge ta da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa Haliru Bello.
Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa Maryam ta daukaka karar ne a ranar Alhamis, mako uku bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke mata hukuncin kisa kan laifin kashe mijinta.
A takardar daukaka karar da ta rubuta wa kotun kan dalilai 20, Maryam, ta bukaci Kotun Daukaka Karar ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a kanta.
Ta yi zargin cewa alkalin kotun Mai Shari'a Yusuf Halilu ya yi hukuncin bisa son rai.
A cewarta hakan ya jawo danne 'yancinta na samun adalci da kuma yanke mata hukunci bisa amfani da hujja ta zahiri.
0 Response to "Maryam Sanda ta daukaka Kara kan hukuncin kisa"
Post a Comment