Gobara ta kona shaguna 77 a kasuwar kurmi dake Kano
Sunday, November 18, 2018
Add Comment
Hukumar kashe gobara ta jahar Kano ta ce: gobara ta kone shaguna 77 a Kasuwar kurmi Kano. Mai magana da yawun hukumar Alhaji Saidu Mohammed ya shaidawa kanfanin dillancin labarai (NAN) ranar lahadi cewa, shaguna 70 ne suka lalace.
"Mun samu sanarwar tashin wutar ne da misalin karfe 07:35 a.m na safiyar lahadi daga bakin Aliyu Ibrahim ta hanyar kiran waya, bamuyi kasa a gwiwa ba muka tura jami'an mu, domin kashe gobarar.
Ya kara da cewa shaguna 70 ne suka rushe a yayin da shaguna 7 suka tsira da taimakon 'yan kwana-kwana.
Yayi kira ga 'yan tireda da mazauna yankin da su rika lura wajen yin anfani da abubuwa wadanda zasu iya haddasa gobara, domin kare sake faruwar hakan a nan gaba.
A karshe yace zasuyi binciken dalilin faruwar gobarar.
0 Response to "Gobara ta kona shaguna 77 a kasuwar kurmi dake Kano"
Post a Comment