Yadda zaka Kare kanka daga kamuwa da cutar Corona virus
Friday, February 28, 2020
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce:
• Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
• Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
• Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
• Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.
Alamomin cutar coronavirus
Wadanne ne alamomin cutar?
Da alama tana farawa ne daga zazzabi, sannan sai mutum ya soma tari.
Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.
Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.