Illolin Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Ga Lafiyar Jiki

Illolin Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Ga Lafiyar Jiki
Magani shine duk abinda idan ya shiga jikin dan adam yake kawo chanjin yanayi cikin kwakwalwa ko jikinsa ta kowani fanni, misali Kamar ta hanyar sha, shafawa, shaqawa, ko ta hanyar yin allura.

Matsalar shaye-shaye a tsakanin al'umma na daga cikin dalilan da su ke haddasa karuwar masu tabin hankali a Najeriya, kamar yadda bincike ya nuna a shekarar 2019.

Ma'aikatar lafiya ta ce akalla akwai masu tabin hankali tsakanin miliyan 40 zuwa miliyan 60 cikin al'ummar kasar da yawansu ya kai miliyan 200, da ke kasar.

Kamar yadda masana suka bayyana shi dai shan miyagun kwayoyi na janyo matsala ga rayuwar mutane musamman ta fannin lafiyar su. 

Miyagun Shaye-shaye:
- Shan maganin da doka ta hana amfani dashi.
- Shan Magani barkatai batare da izinin likita ba.
- Wuce umurnin likita wajen shan magani.

Dalilan Da Suke Sa Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi;
1) Jahilci
2) Matsalolin Rayuwa
3) Al'adu
4) Bangare siyasa
5) Hurda da abokan banza
6) Sakacin iyaye wajen tsawata wa yara
7) Yanayin wurin zama
8) Aikin karfi 

Alamomin Da Ake Gane Mai Shaye-shaye:
1) Rashin nutsuwa
2) Halin lalaci
3) Yawan fushi da rashin hakuri
4) Rashin ladabi, rashin Kunya
5) Yawan abokai daban daban
6) Samun mutun da kayan Shaye-Shayen.
7) Zama cikin kazanta.

Illolin Shaye-shaye:
1) Yawan fadace fadace
2) Rashin nutsuwa a koda yaushe.
3) Talauci
4) Kora daga wurin aiki ko makaranta
5) Yana kawo hatsari ga wanda sukasha suke yin tukin abin hawa
6) Yana kawo ciwon huhu
7) Yana kawo ciwon hauka
8) Yawan tunani mai tsanani da muni.
9) Yana kawo lalacewan mazakuta.
11) Yana kawo lalaci, yadda mai shaye shaye baya iya'yin komai sai yasha kwaya.

Wasu Daga Cikin Hanyoyin Da Za'a bi Dan Maganarce Halayyar Shaye-shaye;
1) Ya zama wajibi iyaye su tashi tsaye wurin kula da tarbiyar 'ya 'yansu, sannan su dinga kula da harkokin su na yau da kullum, su kuma kula da irin abokan da su ke hurda dasu.
2) Dole ne iyaye su kula da irin mutanen da suke shiga da fita a cikin gidajen su, su kuma kula da irin mutanen da iyalan su suke hurda dasu (mata ko maza), saboda yanzu matan aure sun shiga harkan shaye shaye sosai.
3) Dole ne Sarakuna da Malaman Addini su tashi tsaye wurin tsawatarwa da fadakar da Al'ummah bisa illan shaye-shaye ta mahangar addini da rayuwa.
4) Dole ne kuma Al'umma su bada hadin kai wurin taimakawa Jami'an tsaro da jami'an yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi wurin gudanar da ayyukan su!
5) Makarantu da kungiyoyin addini da kungiyoyin sakai, da dukkan Al'ummah dole ne su tashi wurin taima kawa gwamnati da al'umma wurin wayar da kan jama'ah game da illolin shaye shaye.
Allah ka karemu Daga fadawa Cikin wannan hali Mara kyau Amen.
CEO http://admobiblog.com.ng

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel