Garabasa: Yadda Zaka Sayi Datan MTN A Farashi Mai Sauki
Wednesday, July 8, 2020
Add Comment
Layin sadarwa na MTN shi ne mafi shahara cikin layukan wayar sadarwa da aka fi amfani da shi a fadin Nigeria, kamfanin ya kasance yana fito da Sabbin tsaruka domin farantawa masu amfani da layin, a wannan karon ma sunfi to da sabbin tsarika guda 4 waÉ—anda zasu baka damar sayen data akan kudi kalilan, ku biyomu domin sanin yadda tsarin yake.
Yadda Tsarin Yake:-
Da farko dai shi wannan tsarin, ba kowanne layi bane MTN suka bawa damar shiga tsarin ba, saboda haka kana bukar dubawa ko kana daga cikin waÉ—anda suke da damar cin moriyar tsarin.
Yadda Zaka Duba Ko Kana Damar Shiga Tsarin:-
Domin tabbatar da kana daga cikin masu damar shiga tsarin sai ka danna waÉ—annan lambobin *131*65#.
Idan kana da damar shiga tsarin, to zasu baka damar zabar tsarin da kake so ka saya. Idan kuma baka ciki baza su baka wannan damar ba.
Jerin Tsarukan da Adadin Kwanakin Lalacewar su;
1. 250MB @N100 - Kwana 3
2. 1G @N200 - Sati 1
3. 4G @N1000 - Wata 1
4. 2G @N500 - Sati 2
Yadda Zaka Sayi Datan'-
Ga matakan da zaka bi domin sayen datan;
> Da farko ka danna *131*65*, Zasu baka zabi guda 4 na sayen datar sai ka zabi wanda kake so.
> Sai ka tura reply da lambar tsarin da kake so. Misali idan ka zabi 1G akan N200 to lambar tsarin itace 2, to saika shigar da 2 ka tura.
>Da ka tura zasu ce maka zasu dauki kudin datar da ka zaba, sai kayi reply da 1 ka tura.
> Anan zasu baka zabi biyu akan sake saye kamar haka :-
1. Yes (Autorenew):- Idan ka zabi wannan to idan lokacin datar ka ya kare (Expired), zasu saima wani da kansu.
2. No (one_off purchase):- Idan ka zabi wannan to idan lokacin datar ka ya kare, baza su siya ma da kansu, sai dai ka siya da kanka.
Sai ka zabi wanda kake so kayi reply.
> Anan zasu turoma sakon ka sayi Data, sai ka fara amfani da ita.
Yadda Zaka Duda Balance Dinka:-
Domin duba balance dinka sai ka danna wannan lambobin *131*4#.
0 Response to "Garabasa: Yadda Zaka Sayi Datan MTN A Farashi Mai Sauki"
Post a Comment