Kotu ta yanke wa matar da ta jefo mijinta daga bene hukuncin kisa

Wata babbar kotu da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta yanke hukuncin kisa kan matar da ta jefo mijinta daga saman bene.
A ranar Juma'a ne kotun, wacce mai shari'a A T Badamasi ya jagoranta, ta samu Rashida Sa'idu mai shekaru 31 da laifin kashe mijinta Adamu Ali ta hanyar turo shi daga saman bene.
Rashida dai ta jefo mijin nata ne daga kan bene a ranar 20 ga watan fabrairun 2019, a unguwar Dorayi da ke Kano, biyo bayan rikici da ya shiga tsakaninta da shi.
Rikicin ya barke ne bayan da ta ji shi yana waya da wata mace da take zargi budurwarsa ce.
Bayan ta turo shi daga benen ne kuma ya fado ya karye a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Rahotanni dai sun bayyana cewar Rashida na da 'ya'ya biyu da mai gidan nata, sannan ita ce matarsa ta biyu a lokacin da abin ya faru.
Kazalika kafin auren nasu, sun hadu da mijin nata ne a makarantar kwalejin fasaha ta tarayya da ke Kano, ita dalibar Adamu Ali ce, a inda bayan daukar wani lokaci suna soyayya suka yi aure.
Kafin Rashida ta jefo mijin nata Adamu Ali daga kan benen, sai da ta fara kai wa kishiyarta koken, inda ta sanar da ita wayar da ta ji mijinsu yana da budurwarsa, kuma abokiyar zaman nata ta ba ta shawarar barinsa ya ci gaba da wayar, amma ta ki, a cewar rahotanni.
Yanzu dai Rashida na da damar daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da ke Kano nan da wata uku idan har bata gamsu da hukuncin da babbar kotun ta yi mata ba.
An dai fara sauraren shari'ar ne tun a ranar 31 ga watan Mayu 2019.
Ko a watan da ya gabata sai da kotun daukaka kara da ke zaman ta a babban birnin tarayar Najeriya Abuja, ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa bisa kamata da laifin kashe mijinta
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Kotu ta yanke wa matar da ta jefo mijinta daga bene hukuncin kisa"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel