Lionel Messi zai koma bugawa Argentina tamaula

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Argentina, Lionel Messi zai koma buga wa kasar tamaula a karon farko tun bayan gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018.
Kocin Argentina, Lionel Scaloni ne ya tabbatar cewar watakila Messi zai buga wa Argentina daya daga wasan sada zumunta da za ta yi da Venezuela ko kuma Morocco a watan nan.
Rabon da dan kwallon Barcelona ya yi wa Argentina wasa tun fitar da kasar a gasar cin kofin duniya da Faransa ta yi a wasan zagaye na biyu.
Messi shi ne ke kan gaba wajen yawan ci wa Argentina kwallaye da 65 a raga, sai dai yana shan suka cewar kokarin da yake yi a Barcelona ba ya yi wa kasarsa a lokacin tamaula.
Sai dai kuma tawagar Argentina ba ta gayyaci Sergio Aguero da Gonzalo Higuain da kuma Mauro Icardi ba.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Lionel Messi zai koma bugawa Argentina tamaula"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel