Kamfanin jiragen sama na Aero ya kafa dokar hana atishawa a cikin jirgi

Kamfanin jiragen sama na Aero ya kafa dokar hana atishawa a cikin jirgi
Kamfanin jiragen sama na Aero a Najeriya ya kafa dokar haramta wa fasinjoji yin atishawa a cikin jirgi.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a Najeriya, shugaban kamfanin na Aero Kyaftin Ado Sanusi ya ce duk fasinjan da ya yi atishawa cikin jirgin ko da kuwa lafiyarsa lau to za'a killace shi.
Ya ce kamfanin ya tanadi wurin killacewa da kuma jami'ai da za su kula da waÉ—anda aka ga alamar suna da alamomin cutar korona.

Karanta>>> Gwamnatin jahar kano ta dage dokar hana zirga-zirga

Kyaftin Ado ya shawarci matafiya waÉ—anda ba su da lafiya da su zauna gida har sai sun samu lafiya.
A satinnan ne dai ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika ya bayyana ranar ci gaba da sufurin jiragen sama a ƙasar bayan shafe sama da watanni uku jiragen ba sa zirga-zirga. Bbchausa
CEO http://admobiblog.com.ng

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel