Shugaba Muhammad Buhari ya isa Daura gabannin zaben gwamna.
Friday, March 8, 2019
Add Comment
A yammacin ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Daura gabannin zaben gwamna da na majalisar jiha wanda za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Shugaban kasar ya isa Daura a cikin jirgin Shugaban kasa mai saukar ungulu da misalin karfe 6:50 na yamma tare da rakiyar hadimansa da iyalansa makusantansa.
Ya samu tarba daga sarkin Daura, Alhaji Farouk, mataimakansa da kuma daruruwan masoyansa.
0 Response to "Shugaba Muhammad Buhari ya isa Daura gabannin zaben gwamna."
Post a Comment