Za'a Kafa Dokar Fidiye Masu Aikata Laifin Fyade A Jahar Kano

Za'a Kafa Dokar Fidiye Masu Aikata Laifin Fyade A Jahar Kano
Majalisar dokokin jihar Kano ta fara duba yiwuwar sauya dokokin hukunta masu fyade a jihar domin kara tsaurara  su ta yadda idan zai yiwu a riÆ™a fiÉ—iye masu irin wannan laifi.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Hon. Nuradeen Alhassan ne ya gabatar da wannan kudurin, inda ya nemi abokan aikinsa su amince da hukuncin 'fidiya' a kan duk wanda kotu ta samu da laifin fyade.
Ya shaida wa BBC cewa tun da dokar da ake da ita a yanzu ba ta sauya komai ba, lokaci ya yi da za a sauya dokar.
''Mutane gani suke kamar abin wasa ne, domin idan ana zargin mutum da fyade kafin ma a kai shi kotu, zai dauko lauyansa, daga karshe maganar sai ta zama shiririta'' In ji shi.
Bisa dokokin da ake da su a yanzu a jihar Kano, idan kotu ta kama mutum da aikata laifin fyade to zai iya fuskantar daurin shekara 14 ne a gidan yari.
A baya-bayan nan dai hankulan al'ummar Najeriya sun tashi sakamakon ƙaruwar laifukan fyaɗen da ake samu.
Fyaden bai tsaya a kan manyan mata ba, abin harda cin zarafin kananan yara da jarirai.
Rundunar yan sandan jihar kano ta ce sama da kashi 40 na waÉ—anda ake yi wa fyaÉ—en, ana yaudarar sune da kuÉ—i ko abinci, kafin a aikata laifin.
Ya shawarci jama'a da su ƙara sanya ido a kan take-take da kai-komon mutane a yankunansu, domin kare 'ya'yansu da kuma iyalansu.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Za'a Kafa Dokar Fidiye Masu Aikata Laifin Fyade A Jahar Kano"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel