An Kaddamar Da Sabuwar Kungiyar Marubutan Arewa Mai Suna "Arewa Media Writters"

An Kaddamar Da Sabuwar Kungiyar Marubutan Arewa Mai Suna "Arewa Media Writters"
Gabatar Da Sabuwar Kungiyar Marubutan Arewa Mai Suna "AREWA MEDIA WRITERS"

Kungiyar "Arewa Media Writers" Sabuwar kungiya ce da wasu hazikan marubuta daga kowanne yanki dake Arewa cin Nigeria, suka taru suka bude ta, domin bada tasu gudummuwar ga yankin mu na Arewa.

"Arewa Media Writers" kungiya ce mai zaman kanta, bata gwamnati bace, kuma bata 'yan siyasa bace, kungiya ce ta matasa zallah da suka bude ta don cigaban marubutan matasanmu na yankin Arewa masu ta'ammali da kafafan sadarwar zamani.

Zaku iya following/Likes din shafin kungiyar a Facebook https://m.facebook.com/ArewaMediaWriters/

An kafa Arewa Media Writers ne akan kyawawan manufofi kamar haka:


- Zaburar da marubutan yankin mu na Arewa, don ganin sun bada tasu gudummuwar ga al'ummar yankin.
- Hadin kan marubutan yankinmu na Arewa don ganin ana magana da murya daya.
- Isar da sakonnin al'ummar yankin mu na Arewa, zuwa ga masu madafun iko dake yankin
- Yaki da labarun karya ga al'ummar yankin mu na Arewa.
- Sharhi da fashin baki, tare da wayar da kan al'ummar yankin mu game da abunda ya tunkaro yankin namu na Arewa.
- Kare hakki, martabar yankin mu na arewa daga kowanne irin kalubale da ya fuskanto yankin namu.

Karanta>>> Za'a Kafa Dokar Fidiye Masu Aikata Laifin Fyade A Jahar Kano

Haka zalika kungiyar zata zama garkuwar yankin Arewa daga kowanne irin batanci da sharri.

Kungiyar "Arewa Media Writers" ta nada rassa na shugabanci da kuma membobi a dukkannin kananan hukumomi 418 da muke dasu a Arewa cin Nigeria, tare da shugabannin ta a matakin jihohi 19 da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Nan bada dadewa ba kungiyar zata bayyana shugabannin ta, tun daga matakin kasa, jihohi, har zuwa dukkanin kananan hukumomi 418 da muke dasu a Arewa cin Nigeria.

"Arewa Media Writers" tana maraba da dukkanin masu kishin yankinmu na Arewa, da su shigo wannan kungiyar domin bada tasu gudummuwar.

Zaku iya tuntubar shugabannin kungiyar ta email address dinta.

CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "An Kaddamar Da Sabuwar Kungiyar Marubutan Arewa Mai Suna "Arewa Media Writters""

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel