Gwamna Bello Matawalle ya bada gudunmawar naira milliyan 100 domin gina jami’ar musulunci a jahar Zamfara.

Gwamna Bello Matawalle ya bada gudunmawar naira milliyan 100 domin gina jami’ar musulunci a jahar Zamfara.
Matawalle ya mika wannan kudi ne a lokacin da shugabannin kungiyar Jama'atul Izalatil Bida Wa Ikamatussunnah, JBWIS karkashin shugabancin Sheikh Bala Lau suka Kai masa ziyara a garin Gusau.
Ya yi kira ga gwamnoni da attajirai musamman na yankin Arewa su bada gudunmawar su domin samun nasara wajen gina wannan jami'a ta musulunci.
Jaridar Premium time ta ruwaito cewar, Matawalle ya koka kan matsalolin rashin ilimi da tarbiyya da ya yiwa yara yanzu yawa musamman a yankin Arewa.
"Mun koma wadanda basu kwaunar juna da kishin yankin mu. Ba mu son juna. Yanzu ya kai ga a yankin mu na Arewa nan ne ayyukan ta'addanci ya fi tsanani saboda yadda kauna da son juna ya fita daga zukatan mu.
" Ku duba yadda matsalar ' yan bindiga ya fi karfin mu a Arewa, Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a tsakanin mu, sace-sace, Kashe-kashe da ba a san mu da shi ba duk yanzu sune muke fama da su saboda kiyayar da ta shiga tsakanin mu.
"Na Yi kokari wajen dawo da zaman lafiya a jiha ta Zamfara kuma zan da ge domin maida hankali akan haka domin mutanen mu koma cikin walwala kamar yadda muke ciki a da.
Ya kara da cewa " Yanzu rokona gareku shine ku ci gaba da fadakar da iyaye wajen kula da tarbiyyar 'ya'yan su sannan kuma ku malamai ku maida hankali wajen ilmantar da yara yadda ya kamata.
A jawabin sa jagoran tawagar, kuma shugaban kungiyar JIBWIS, Sheikh Bala Lau ya ce kungiyar ta kawo wa gwamnan jihar ziyara ne bayan duba wani makaranta da tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya ba kungiyar JIBWIS a garin Shinkafi. 
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Gwamna Bello Matawalle ya bada gudunmawar naira milliyan 100 domin gina jami’ar musulunci a jahar Zamfara."

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel