Yadda Zaka Turawa Wani Data A Layinka Na MTN

Yadda Zaka Turawa Wani Data A Layinka Na MTN
A yau a wannan rubutun zamu nuna muku yadda zaku tura kyautar Data ga abokai, 'yan uwa, da kuma masoyanku

Data ta kasance mahadi ga wayoyin hannu da kuma komfutoci, wadda take bada damar ziyartar yanar gizo a wannan zamani, kamfanin layin sadarwa na MTN yana daga cikin kamfanonin sadarwa masu yin kasuwancin wannan Data, domin samarwa kostomomin su damar shiga yanar gizo da kuma yin hira da abokai a shafukan sada zumunta na zamani kamar: Facebook, Twitter, WhatsApp, LinkedIn da sauransu.

Muhimman cin da data ta ke dashi yasa kamfanin layin sadarwa na MTN ya fito da tsarin tura data izuwa wani layin na MTN, wanda a wannan rubutun zamu yi bayanin yadda zaka tura kyautar Data ga 'yan uwa da abokai.

• Yadda Zaka Tura Kyautar Data Zuwa
Wani;-

Ita wannan hanyar anayin ta ne idan kana da data a layin ka.

> Da farko ka danna *131*7#  sai ka tura zasu baka zabi kamar haka:-

1. Transfer from data balance
2. Buy for a friend
3. Request from a friend
4. View pending request

> Sai ka danna 1 ka tura zasu baka inda zaka sa lambar waya
> Sai ka shigar da lambar wanda zaka turawa
> Sai ka zabi adadin MB din da zaka tura, sai ka danna lambar jerin sa ka tura
> Sai ka dannan 1 ka tura 
> Daga nan zasu turoma sakon cewar sun tura datar shikenan.

Karanta>>> GARABASA: Yadda Zaka Sayi Datar MTN A Farashi Mai Sauki

• Yadda Zaka Sai Wa Wani Data Ta Layin ka Na MTN;-

Shi wannan tsarin yana bayar da damar sai wa abokai data ne kai tsaye.

> Da farko ka danna *131*7#  sai ka tura zasu baka zabi kamar haka:-

1. Transfer from da
2. Buy for a friend
3. Request from a friend
4. View pending request

> Sai ka danna 2 ka tura zasu baka inda zaka sa lambar waya
> Sai ka zabi plan din da zaka siya masa sai ka tura jerin lamar tsarin
> Sai ka zabi adadin MB din da zaka siya masa sai ka tura jerin lambar tsarin.
> Sai ka dannan 1 ka tura 
> Daga nan zasu turoma sakon cewar sun tura datar shikenan

• Yadda Zaka Nemi Abokinka Ya Turama Data;-

Wannan tsarin zai baka damar turawa abokinka sakon ya siya/turamin data, ga yadda zaka yi;

> Da farko ka danna *131*7#  sai ka tura zasu baka zabi kamar haka:-

1. Transfer from data balance
2. Buy for a friend
3. Request from a friend
4. View pending request

> Sai ka danna 3 ka tura zasu baka inda zaka sa lambar waya
> Sai ka shigar da lambar wanda kake so ya turo/siya ma data sai ka tura
> Daga nan zasu tura mada sakon cewar kana bukatar ya siya/turama Data.

• Yadda Zaka Gane Ko Wani Ya Turoma Sakon Ka Siya/Tura mashi data;-

> Ka danna *131*7# sai ka tura
> Sai ka dana 4 sai ka tura, zasu nuna ma sakon waÉ—anda suka bukaci ka siya musu data.

Ka tuna: Sau biyu ake iya tura data a rana, kuma adadin datar da za'a tura a rana shine 200MB.

CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Yadda Zaka Turawa Wani Data A Layinka Na MTN"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel