Majalisar Dokokin jihar Kano zata kirkiro sabbin masarautu guda Hudu
Monday, May 6, 2019
Add Comment
Majalisar dokokin jihar Kano ta fara sauraren wani kudurin dokar da ya bukaci kafa wasu karin masarautu hudu a jihar.
Rahotanni sun ce masarautun da ake son kirkirowa sun hada da masarautar Rano da Gaya da Bichi da kuma Karaye, kuma daraja ta daya ake son ba su.
Wannan dai wani yunkuri ne da ake dangantawa da kokarin rage karfin ko karya lakwan masarautar Kano.
Hakazalika, akwai wadanda suke ganin hakan ba ya rasa nasaba da rashin jituwa da ake ganin akwai tsakanin gwamnan jihar Kanon Abdullahi Ganduje da kuma Sarki Muhammadu Sunusi na Biyu.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Kanon, Baffa Baba Danagundi ya shaida cewa BBC cewa tun kafin kungiyoyin sun mika takarda bukatar karin wadanan masarautu dama a baya sun yi nazari kan dokar majalisar masarautar kan kwaskwarimar dokar da ake bukata.
"Don haka kusan wannan kiraye-kiraye ya zo ne a kan gaba domin samar da ingancin tsaro da gyara al'adu da masarautun Kano," in ji Danagundi.
Dan Majalisar ya kuma ce bukatar karin masarautu hudu da aka gabatar yana iya yiwuwa a amince ko a rage ko a kara, "amma dai ya ta'alaka da yadda ta kama da shawarwarin da kwamiti da amintar majalisa."
BBC
0 Response to "Majalisar Dokokin jihar Kano zata kirkiro sabbin masarautu guda Hudu"
Post a Comment