Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da za'a fara jarrabawar WAEC ta shekarar 2020
Monday, July 6, 2020
Add Comment
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana ranar da za'a fara jarrabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC ta shekarar 2020.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa karamin Ministan Ilimi na Najeriya Emeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen taron kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 a Abuja.
Ya ce "za a yi jarrabawar ne daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumban 2020.
Emeka Nwajiuba ya ce, "Za a fara jarrabawar daga 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba 2020.
''Mun yi iyakar yin mu kuma mun tattauna da wakilanmu a WAEC yau da rana, mun tabbatar da ranakun cewa za a yi jarrabawar ne daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba.
"Daga gobe, za mu tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar, duk za su halarci taron na gobe.
0 Response to "Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da za'a fara jarrabawar WAEC ta shekarar 2020"
Post a Comment