Bayanin Shugaba Muhammadu Buhari Akan Tsaron Kasa

Yau ne ranar Demokaradiyyah a gurin attajirai da manyan 'yan siyasar Nigeria, a gurin talaka har yanzu ba su san dadin dandanon romon tsarin mulkin Demokaradiyya da ake sha a Kasar ba

Shugaba Buhari ya gabatarwa da jawabin ranar Demokaradiyyah safiyar yau din nan, ga fassaran jawabin da yayi akan batun tsaron Kasar:

"Ina cikin nadama da bakin cikin asarar rayuka da aka yi a kwanan nan a jihar Borno da Katsina, jami'an tsaro zasu kawo 'karshen wadannan miyagun mutanen, kuma zan tabbatar da nayi adalci..

"Ina mika ta'aziyya ta zuwa ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukan su a kwanakin nan, in sha Allahu zan cigaba da tilasta jami'an tsaro su tsare rayukan mutane, musamman wadanda suke zaune a karkara, ina bada hakuri akan abubuwan da suka faru...

"Nigeria ta shiga cikin matsaloli masu yawa ada da yanzu, kuma ada 'din ta fita daga matsalar tayi karfi daga baya, da ikon Allah zamu yi nasara akan wannan matsalar ta tsaro dake addabar mu a yanzu..

"Na bayar da umarni a bude sabon shiri domin rage matsalolin matasa, kowace karamar hukuma za'a dauki mutane dubu daya (maza da mata) kuma wannan aikin an fara shi daga yanzu, na bada umarni a fara shi ~jawabin shugaba Buhari a yau

Yaa Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Ka bashi ikon aikata daidai, Ka fitar da Nigeria daga matsalolin da suke damunta Amin

CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Bayanin Shugaba Muhammadu Buhari Akan Tsaron Kasa"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel