Messi da Luis Suarez za su taka leda a karawar Barcelona da Mallorca
Saturday, June 13, 2020
Luis Suarez da Lionel Messi na cikin 'yan wasan da za su buga wa Barcelona tamaula a yayin da jagorar La Liga za ta fafata da Mallorca ranar Asabar.
Dakatar da Gasar da aka yi sakamakon annobar korona ta bai wa Suarez, mai shekara 33, damar murmurewa bayan dan wasan na Uruguay ya yi jinyar tiyatar da aka yi masa a watan Janairu.
Messi ya ji rauni a cinyarsa amma dan wasan na Argentina, mai shekara 32, ya koma atisaye a makon nan a yayin da Barca take shirin buga wasanta na farko bayan kwana 97.
"Yana cikin hali mai kyau kuma ba zai fuskanci wata matsala ba," a cewar koci Quique Setien.
A game da Suarez kuwa, ya kara da cewa: "Ya samu sauki fiye da yadda muka yi tsammani. Abin tambayar kawai shi ne, wanne irin shiri ya yi bayan ya kwashe tsawon lokaci bai buga kwallo ba, sannan kuma shin yana shirye ya koma kwallo."
Shi ma Samuel Umtiti ya samu sauki amma an dakatar da Clement Lenglet domin dan wasan Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 21, ya iya samun damar buga wasansa na biyu a Barca.
Real Madrid ta sha gaban Barca a saman tebur lokacin da suka doke su da ci 2-0 a Bernabeu ranar 1 ga watan Maris.
Sai dai Barca ta koma ta daya a saman tebur ranar 7 ga watan Maris lokacin da Messi ya ci bugun daga Kai sai mai tsaron gida - wanda shi ne na 19 da ya ci a kakar wasan bana - inda suka tashi da ci 1-0 a gida a wasansu da Real Sociedad, yayin da Real ta sha kashi da 2-1 a wasanta da Real Betis washegari.
Barca tana da tazarar maki biyu a saman tebur yayin da ya rage mata saura wasa 11 a Gasar La Liga, wanda aka koma ranar Alhamis inda Sevilla ta doke Betis a wasan hamayya.
Mallorca ita ce ta ukun karshe a tebur bayan ta doke Eibar da ci 2-1 a wasan karshe kafin a dakatar da gasar sakamakon annobar Corona.