Abubuwan da yakamata kasani ga me da N-Power
Monday, June 22, 2020
Al'umma sunayin tambayoyi ga me da shin me shaidar kwalin SSCE zai iya cikewa?
Ga yadda tsarin N-power yake :
1- N-power Agro
2- N-power Tax
3- N-power Build
4- N-power Health
5- N-power Teach
1- N-power Agro:
Wannan tsarin ana bukatar masu shaidar kwalin Diploma, HND da Degree, kuma wanda suka karanci fandin Agric ko Nutrition.
2- N-power Tax
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin HND da Degree ne kaÉ—ai, Kuma wanda suka karanci fannin Finance, Economic, ko Accounting.
3- N-power Build
Wannan tsarin suna buƙatar masu shaidar karatun SSCE, Diploma, HND da Degree, bugu da kari wanda bashi da takardan shaidar karatu ma zai iya cikewa.
4- N-power Health
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin Certificate, Diploma, HND da Degree.
Daga cikin wadanda suke bukata akwai:
- Midwives
- Nursing
- Medical Record
- CHO, CHEW, JCHEW
- PHARMACY
- Biology
- Biochemistry
- Health education
- EHO, EVT, EHA
5- N-power Teach
Wannan tsarin suna bukatar masu kwalin NCE, Diploma, HND, da degree.
Ku share domin al'umma su samu damar shiga tsarin.
Allah Ubangiji Ya bawa kowa sa'a.