Gwamnatin Saudiya ta sanar da adadin mutanen da zasu gudanar da aikin hajjin bana
Tuesday, June 23, 2020
Gwamnatin Saudiya ta ce, kimanin mutane dubu goma 10,000 ne kacal da ke zaune a cikin kasar za su gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar coronavirus da ta tilasta rage yawan maniyata.
Ministan Kula da Aikin hajji na kasar, Mohammed Benten ya sanar da haka ga mane ma labarai a birnin Riyadh, yana mai cewa adadin mahajjatan na bana ka iya Zama Kasa da dubu goma.
Karanta>> Abubuwan da yakamata kasani ga me da N-Power
Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin kasar ta bada tabbacin cewa, za a gudanar da aikin hajjin bana, amma ga mutanen da ke zaune a cikin kasar, ma'ana dai, ban da baki daga kasashen ketare.
Tuni al'ummar Musulmi daga sassan duniya suka fara mayar da martani, inda wasu ke bayyana rashin jin dadinsu da matakin hana dimbin Musulmai sauke farali a bana.
A kowacce shekara dai, ana samun a kalla Musulmai miliyan biyu da ke gudanar da aikin hajji a kasar Saudiya. rfi.fr