Kotun Koli Ta Rushe ‘Yan Takarar APC A Zamfara, Ta Ba PDP Kujerar Gwamna

Babbar kotun kolin Nijeriya ta ce jam’iyyar APC ba ta yi zabukan fitar da gwani ba, don haka jam’iyyar da take bin APC a yawan kuri’u ita ce ta lashe zabukan jihar da aka yi a watan Maris. A zaman kotun na ranar Juma’a ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba gabanin babban zaben shekarar 2019 a jihar. Hukuncin kotun ya jaddada hukuncin da kotun daukaka kara a jihar Sakkwato ta yanke, wadda ita ma ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jihar. Kotun kolin ta ce jam’iyyar ba ta da halatattun ‘yan takara don haka ba za ta iya kasancewa wadda ta lashe zabukan jihar ba.
Tun farko dai Sanata Kabiru Marafa ne ya fara shigar da kara a gaban kotu, inda ya kalubalanci zaben fidda gwanin da APC ta yi. Jam’iyyar adawa ta PDP a shafinta na Twittwr ta wallafa hoton wanda ya yi mata takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar, inda ta ce dimokradiyya ta yi nasara.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Kotun Koli Ta Rushe ‘Yan Takarar APC A Zamfara, Ta Ba PDP Kujerar Gwamna"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel