Zanyi Iya Kokari na Wajen Kyautatawa ‘Yan Nijeriya – Shugaba Buhari

A jiya Litinin ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin yin iyakan kokarinsa na ganin ya kyautata wa dukkan yan Nijeriya a karon mulkinsa na biyu. Ya kuma bayar da tabbacin cewa, zai yi aiki tukuru na ganin ya samar wa Nijeriya makoma na gari tare da dukkan yan Nijeriya gaba daya a yayin da ya fara zagaye na biyu na wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu 2019, ya kuma mika godiya ga dukkan jama’ar da suka zabe shi a zaben da aka gudanar kwanan nan. Shugaba Buhari ya yi wannna bayanin ne a yayin da yake karbar bakoncin mambobin kwamitin amintattun kungiyar Gidauniyar Jihar Katsina (Katsina State Debelopment Fund) karkashin jagorancin Maishari’a Mamman Nasir a fadar shugaban kasa dake Abuja. Shugaba Buhari ya kuma kara cewa, zagayen yakin neman zaben da ya yi a fadin tarayyar kasa nan ya taimaka masa na sanin halin a kasar ke ciki. A sanarwar da jami’in watsa labaransa Mista Femi Adesina ya sanya wa hannu, Buhari yan kuma bayyana cewa, “ina matukar godiya a bisa goyon bayan da kuka bani, zan kuma yi iyakan kokarin na a zangon mulki na biyu. Za mu yi wa Nijeriya da ‘yan Nijeriya aiki yadda ya kamata.” Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, jama’ar da suke halartar yakin neman zabensa a zagayen a ya yi sun fi karfin a ce ana basu kudi ne ko kuma yaudarar su ake yi, ya ce wannan yana faruwa ne saboda yarda da amincewa da suke yi masa a kan mulkin da yake yi musu.Shugaba Buhari ya kuma lura da cewa, shi ne shugaban gidauniyar Ilimi ta jihar Katsina na tsawon shekara 17, inda aka samu gaggarumin gudumawa a bangaren ilimi da harkar lafiya da aikin gona a fadin jihar, inda talakawa suka amfana matuka. A martaninsa, Galadiman Katsina, Mai Shari’a Nasir, ya ce, gidauniyar na mika godiyarta ga dukkan ‘yan Nijeirya a bisa zaben shugaba Buhari da suka yi a karo na biyu. “Muna godiya ga Allah da ya sake bamu nasarar sake zabar Shugaba Buhari a karo na biyu, muna murna tare da godiya ga yan Nijeriya da suka sake zabar ka a karo na biyu,’’ inji shi. Maishari’a Mamman Nasir ya kuma ce, suna godiya da irin ayyukan da Shugaban kasar ya yi a lokacin yana jagorantar gidauniyar. Source Leadership
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Zanyi Iya Kokari na Wajen Kyautatawa ‘Yan Nijeriya – Shugaba Buhari"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel