Gwamnatin Tarayya Da ASUU Sun Dawo Teburin Tattaunawa.
Thursday, March 28, 2019
Add Comment
Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’a ta ASUU sun fara wani sabon zagayen tattaunawa a kan yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2009. Shugaban kwamitin tattaunawar daga bangaren gwamnatin tarayya, Farfesa Babalakin ya bayyana haka a tatauwarsa da ‘yan jarida a garin Abuja jiya Laraba bayan wani dogon tattaunawa da suka yi na tsawon awa 6, ya ce, lallai a kwai alamun nasara a tattaunawar da suke yi da bangaren malaman. Babalakin ya kuma kara da cewa, kungiyar ASUU sun gabatar da bukatu 20 da suke bukatar a tattauna tare da amincewa da su don a samu dorewar zaman lafiya a jami’o’inmu. Ya kuma kara da cewa, dukkan bangarorin suna da karin gwiwar kawo karshen dukkan matsalolin dake fuskantar bangaren ilimi na Nijeriya gaba daya.
0 Response to "Gwamnatin Tarayya Da ASUU Sun Dawo Teburin Tattaunawa."
Post a Comment