Shugaba Buhari Ya Dakatar Da Hakar Ma’adanai A Jahar Zamfara.
Monday, April 8, 2019
Add Comment
Shugaban kasar Nijeriya, Muhammad Buhari, ya dakatar da dukkanin aikace-aikacen hakar ma’adanan kasa a jihar Zamfara nan take ba tare da bata wani lokaci ba. Kana ya umurci Turawan da su ke wuraren hakar Ma’adanai a jihar da su gaggauta tashi kana jami’an tsaron Puff-Adder za su amshi wuraren hadi da mamaye dukkanin wuraren da a ke hakar ma’adanai a jihar ta Zamfara.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa, mai bai wa Shugaban kasar Nijeriya shawara kan kafafen sadarwar zamani, Bashir Ahmad, shi ne ya shaida hakan a shafinsa na Twitter a jiya Lahadi. Ya ce, “Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin dakatar da dukkanin hada-hadar hakar albarkatun da ma’adanan kasa a jihar Zamfara nan take ba tare da bata lokaci ba. Bashir ya kara da cewa, “Sannan kuma bayan dakatar da aikin hakar ma’adanai, gwamnatin tarayya ta umarci dukkanin ‘yan kasar waje da su ke yankunan da a ke hakar ma’adanai da su bar wuraren cikin gaggawa. Sannan, an umurci rundunar musamman ta samar da zaman lafiya ta ‘Puff-Adder’ ta amshi wuraren nan take.” Sai dai kawo yanzu, shugaban kasa bai bayyana dalilin daukar wannan matakin ba, sai dai a na hasashen matsalolin tsaro da su ke kara addabar jihar Zamfara ne ya sanya gwamnatin tarayya daukar wannan matakin.

0 Response to "Shugaba Buhari Ya Dakatar Da Hakar Ma’adanai A Jahar Zamfara."
Post a Comment