Barcelona Ta Lallasa Atletico Madrid da ci 2-0


Barcelona ta bayar da tazarar maki 11 a saman teburi bayan 2-0 da ta ci Athletico Madrid a zazzafan wasan hamayya da suka buga a daren yau Asabar. Luis Suarez da Lionel Messi ne suka ci wa Barce kwallaye masu kyan gaske, wanda ya kara dora su a hanyar lashe kofin La Liga na biyar cikin shekaru bakwai. Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a kori tsohon dan wasan Chelsea Diago Costa bayan ya ci mutuncin alkalin wasa Jesus Gil a minti na 27. Su kuwa Suarez da Messi ba su bari damar ta kubuce ba. Suarez ne ya fara jefa kwallo ana saura minti biyar a tashi daga wasan, inda Messi ya ci kwallo ta biyu dakika 60 bayan haka a minti na 86.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Barcelona Ta Lallasa Atletico Madrid da ci 2-0"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel