Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Gwamnoni akan batun Karin albashi.
Monday, November 19, 2018
Add Comment
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari akan batun karin karancin albashin ma'aikata wanda aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja.
Gwamnoni hudu da suka halarci ganawar sirri sun hada da: Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode, Gwaman Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari .
A makon da ya gaba ta ne Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi. Bayan wani tattaunawa da qungiyar Gwamnonin ta yi da kungiyar kwadago, wanda hakan yasa Gwamnonin suka mayar wa kungiyar martani akan cewa, ko dai a amince da albashin naira dubu 30 ko kuma a ajiye aiki.
0 Response to "Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Gwamnoni akan batun Karin albashi."
Post a Comment