Amita Bachchan ya biyawa manoma bashin dala dubu 500
Wednesday, November 21, 2018
Add Comment
Fitaccen jarumin fina-finan Bollywood Amita Bachchan, ya biya wa wasu manoma bashin da ake binsu fiye da dala dubu 500.
Jarumin ya bayyana hakan ne a shafinsa na intanet a ranar Talata, inda ya ce manoman da ya biyawa bashin sun kai 1,398.
Wadannan manoma dukkaninsu sun fito ne daga jihar Uttar Pradesh, wato mahaifar jarumin.
Bangaren aikin noma ya na samun koma baya a kasar ta India, inda a wasu lokutan ba a fiye samun amfani mai yawa ba.
An kiyasta cewa tun daga shekarar 1995, manoma akalla dubu 300 sun kashe kansu a kasar ta Indiya, saboda dumbin bashin da ake binsu.
Yawanci dai manoman na ciwo bashin ne daga bankunan kasar domin yin noman, amma a karshe sai su ka sa biyan bashin da suka karbo a bankunan.
0 Response to "Amita Bachchan ya biyawa manoma bashin dala dubu 500"
Post a Comment