Gwamnatin Jihar Kano ta Dage Dokar Hana Zirga-Zirga

Gwamnatin Jihar Kano ta Dage Dokar Hana Zirga-Zirga

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya janye dokar kulle da ke aiki a jihar.
Ma'aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter ranar Alhamis.
Gwamnatin ta ce ma'aikata daga mataki na 12 zuwa sama za su koma aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli.
Sannan ana ci gaba da tattaunawa kan ranar da za a bude makarantu ga dalibai da ke shekarar karshe da masu rubuta jarrabawar kammala aji uku da 'yan firamare masu rubuta jarabawar shiga sakandare.

Karanta>>> Jerin sunayen mutanen da shugaba Buhari yake son nadawa a matsayin Sabbin Jakadu

Haka zalika cire wannan doka na nuni da cewar an bude dukkan guraren da aka kulle a baya amma dole su tabbatar da matakan kariya a guraren harkokinsu kamar yadda hukumomin lafiya suka umarta, a cewar kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba. bbchausa
CEO http://admobiblog.com.ng

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel