Wakata ta taba sanadiyar ceto rai da sulhunta ma'aurata - Nura M Inuwa
Thursday, June 18, 2020
Nura M Inuwa, fitaccen Mawaki Wanda ya shahara wajen yin wakokin zamani, ya yi wakoƙin soyayya, siyasa, aure da kuma yabo da dama.
A tattaunawar da BBC ta yi da shahararren mawaƙin a Shafin Instagram da Facebook, mawaƙin ya ce ya fara waƙa ne tun a shekarar 2007, kuma ya fara ne da waƙar siyasa.
Ya bayyana cewar, a halin yanzu waka ta zama sana'a, sannan hanya ce da za'a iya isar wa da mutane sako musamman idan aka ga É“arna sai a gyara.
Ya ce wakokinsa da dama sun kawo sauyi, domin akwai wata waƙarsa mai suna 'Ga Wuri Ga Waina' wadda a ciki ne ya yi magana kan makomar wanda ya kashe kansa.
Ya ce a sakamakon haka "akwai waɗanda suka kira ni suka ce na yi ceto, ma'ana na ƙwaci wata yarinya daga halaka, tana ƙoƙarin halaka kanta da ta ji waƙar 'Ga Wuri Ga Waina' sai ta fasa halaka kanta".
Mawaƙin ya ce akwai waƙarsa ta Tambihi wadda a sakamakon haka ne wani mahaifi da ya yi niyyar yi wa 'yarsa auren dole ya janye kudurin nasa.
A irin waƙoƙi masu isar da saƙo dai da Nura ya yi akwai ta 'Dafin So' wadda ya ce "a waƙar na yi maganganu daban-daban wanda akwai wanda ya kira ni ya ce a dalilin wannan har ya yi fushi matarsa har ta yi yaji, don haka abin da na faɗi a cikin wakar na matsayin da so yake da shi, hakan ya sa suka yi sulhu a tsakaninsu ya dawo da abarsa."
Nura ya bayyana cewa duk a cikin waƙoƙi ya fi son waƙar soyayya, sakamakon babu abin da ya fi so fiye da soyayya a rayuwarsa.
Ya bayyana cewa ya yi waƙoƙi da dama tun bayan da ya fara waƙa, amma waƙar Rigar Aro ita ce bakandamiyarsa.
A hirar da BBC tayi da shi, ya bayyana dalilin da ya sa ba a cika ganinsa a cikin fina-finan Hausa ba, ya ce "ni mutum ne wanda ina so in ɗauki layi guda ɗaya, in ba shi ƙarfi, ni shi na zaɓa, ni ba ni da ra'ayin fim".