Sharuda takwas da kasar Saudiya ta gindaya domin gudanar da aikin hajjin bana

Sharuda takwas da kasar Saudiya ta gindaya domin gudanar da aikin hajjin bana
Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar da sharudda guda takwas da suka shafi aikin hajjin bana 2020 a wata sanarwa a ranar Talata.
A ranar Litinin ne Saudiyya ta sanar da cewa mazauna kasar ne kadai - cikin su har da 'yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta - za a bari su yi aikin Hajjin bana.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar aikin Hajji kasar ta fitar ta ce sun dauki mataki ne bisa la'akari da yadda cutar korona ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya.

Karanta>> Gwamnatin Saudiya ta sanar da adadin mutanen da zasu gudanar da aikin Hajjin bana

Ga jerin sharuddan kamar yadda ma'aikatar ta fitar:
1. Za a yi wa alhazan gwajin cutar korona kafin su fara aiki, sannan za a killace su bayan an kammala aikin.
2. Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana.
3. Ba za a bar utanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba. 
4. Za a dinga sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.
5. Za a dinga gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-dkadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna. 
6. Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura 10,000 ba.
7- Babu wanda zai je Saudiyya don yin aikin hajji daga wasu kasashen. 
8  Za a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa. BBC

CEO http://admobiblog.com.ng

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel