Kullu Nafsin Za'iqatul Maut, Allah ya yiwa Admin Secretary na Kungiyar IZALA Rasuwa
Thursday, June 11, 2020
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN
Allah ya yiwa Malam Mukhari Ibrahim (Vom) Rasuwa. Malam Mukhtari shine Babban Admin Secretary na kungiyar IZALA.
Za'a gabatar da sallar janazar sa a masallacin Juma'ah na JIBWIS dake Gwallaga a cikin garin Bauchi da misalin karfe daya na rana 1:00pm yau Alhamis insha Allah, kamar yadda mataimakin shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe ya sanar.
Allah ya jikansa yayi masa rahama amen
JIBWIS NIGERIA
10-06-2020