Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar daukan sababbin ma'aikatan N-Power

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar daukan sababbin ma'aikatan N-Power
Ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa za'a sallami matasan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 da kuma 2018 wannan watan na Yuni, 2020.

Shirin N-Power ya dauki matasa kimanin 500,000; a karon farko an debi mutane 200,000 a Satumba 2016, sannan aka sake dibar 300,000 a watan Agustan, 2018.

A lokacin da aka daukesu aiki, an bayyana musu cewa watanni 24 za suyi amma matasa 200,000 farko da aka dauka sun kwashe sama da 40,000.

Karanta>> Nigeria ta samu Karin mutumm 667, wadanda suka kamu da coronavirus


A wani jawabi, Ministar ta ce gwamnatin tarayya ta fara shirin mayar da su wani shirin aikin hannu.

Ta Kara da cewa: "Mun kaddamar da mayar da matasan diban farko da na biyu cikin wasu shirye-shiryen aikin hannu da gwamnati ta shirya tare da hadin gwiwar  wasu kamfanoni masu zaman kansu domin daukan matasan aiki.."

"Gwamnatin tarayya za ta cigaba da fadada shirin na  N-Power, kuma yanzu zamu fara daukan sababbin matasa."
"Saboda haka, ma'aikatar na sanar da cewa yan diban farko zasu tafi a ranar 30 ga Yuni, 2020 yayinda diba na biyu zasu tafi 31 ga Yuli, 2020."

Ma'aikatar ta ce za'a fara sabon dauka ne daga ranar 26 ga Yuli, 2020.
Za'a bude shafin yanar gizon yin rijista daga ranar 26 ga Yuni, 2020 domin masu bukata su nema.

N-Power shiri ne da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar a shekarar 2016 karkashin ofishin jin dadin al'umma.

An samar da shirin ne domin rage yawan matasa marasa aikin yi a Najeriya da kuma rage talauci.

CEO http://admobiblog.com.ng

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel