Banji dadin Abinda Yan Kwankwasiyya Suka Yi Wa Sheik Pantami – Dr Rabi'u Musa Kwankwaso

Shugaban kungiyar Kwankwasiyya Dr Rabi'u Musa Kwankwaso ya fito fili a shafin sa na sadarwa ya yi magana kan abunda ya faru tsakanin magoya bayansa da kuma Ministan sadarwar Nijeriya Dr Isah Pantami.
Kwankwaso yace "Na kalli bidiyon abunda ya faru, sai dai na lura da cewa daga cikin magoya bayanmu na Kwankwasiyya akwai wadanda suke kokarin daukar hoton Selfie da Malam, akwai kuma wasu batagarin da suke masa ihun ba ma so"
Sabanin yadda wasu daga cikin 'yan Nijeriya suka dunga runtse ido suna yi wa Kwankwasiyya tofin tsinuwa gaba daya.
Har a cikin turken zuciyata bana goyon bayan abunda 'yan Kwankwasiyya suka yi wa Malam, sai dai kuma ba zan yi wa Kwankwasiyya tare da magoya bayan ta tofin tsinuwa ba.
Abunda ya faru tsakanin Malam da 'yan Kwankwasiyya tamkar abun ya faru ne kamar wasu suna jiran irin haka don su ciwa Kwankwaso da Kwankwasiyya mutunci.
Mun sani cewa taron da 'yan Kwankwasiyya suke yi a filin Malam Aminu Kano kafin zuwan Malam abune na murna da farin ciki, wanda kaf a yankin Arewa ba kasafai ake samun shugabannin da suke irin wannan kokari ba.
Wasu marubuta da kuma mabiya wasu bangarori na siyasa da ra'ayinsu ya sha daban da na Kwankwaso sun yi amfani da wannan dama wurin ci masa zarafi da kuma kushe aiyukkansa ga baki daya.
Zan so jama'a ku fahimci cewa komai adawar da kake da mutum idan matsala ta samu ka tsaya ka yi masa adalci, domin kada ka zama jigon haifar da wata tarzoma da za ta iya wuce tarzomar da kake kokarin kashewa.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Banji dadin Abinda Yan Kwankwasiyya Suka Yi Wa Sheik Pantami – Dr Rabi'u Musa Kwankwaso"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel