Abubuwan da ake bukata don shiga shirin N-power 2020 a saukake.

Abubuwan da ake bukata don shiga shirin N-power 2020 a saukake.
1. SHEKARU SU ZAMA 18-35 (WANDA AKA HAIFA 1985 ZUWA 2002)

2. BVN (22....) LAMBAR BANKI

3. EMAIL (MAI AIKI WANDA ZAKA IYA BUDE SHI KAGA SAKO) KO KUMA LAMBAR WAYA MAI AIKI WADDA SAKO YAKAN SHIGO.

4. HOTO PASSPORT WANDA BAI HAURA 1MB BA (JPEG FORMAT)

5. TAKARDAR SHAIDAR GAMA MAKARANTA (DEGREE CERTIFICATE) DA SHAIDAR GAMA BAUTAR ƘASA (NYSC CERTIFICATE) AMMA WANNAN GA IYA WANDA ZASU SHIGA TSARIN N-TEACH DA N-HEALTH NE KAWAI

YADDA AKE REJISTA A SAUKAKE
1. Da farko zaka shiga Shafin www.npower.fmhds.gov.ng don fara yin rejista da kanka idan zaka iya. Amma ka tabbata kayi scanning abubuwan da muka fada a sama da wayarka ko a computer. A waya zaka iya downloading camscanner a Google play store domin yin scanning din takardun ka da hoton ka da id card dinka.

2. Kana bude Shafin, zaka ga dokoki da ƙaidoji NPower, sai ka cike cewa ka yarda sai ka tafi shafi na gaba

3. Shafi na gaba zaa bukaci ka shigar da email dinka mai aiki ko kuma lambar wayarka wadda kake amfani da ita, sai ka shigar ba bata lokaci

4. Daga nan za'a bukaci da ka shiga asusunka na email don ka tabbatar da cewa kai ne, inda zaka tura maka da link sai ka danna shi, ka jira daga nan zai tabbatar da cewa kaine.

5. Da zarar an tabbatar da email dinka, to zaa bukaci ka shigar da lambar ranar haihuwar ka (dd/mm/yyyy) da BVN dinka wadda take guda 11 ce, idan BVN dinka ba dai dai bace, to bazaa barka ka wuce wannan bangare ba. (idan baka san Bvn dinka ba, zaka iya danna *565*0# a layinka na MTN wanda kake amfani dashi a banki, zasu cajeka N20 amma zasu turo maka da BVN dinka ta gaske)

Karanta>>> Mutane sama da 22,000 ne suka kamu da cutar korona virus a Nijeriya


6. Za'a bukaci ka shigar da sunanka a jere ( Surname, first name, middle name) kamar yadda yazo a BVN dinka, don haka yana da kyau mutum yasan a yaya suka jera su a ID card dinsa wanda yayi amfani dashi a banki

7. Bangaren karatu (educational background and program page) zaa bukaci ka tabbatar da cewa kayi karatu ko bakayi ba, ka fadi matakin karatun ka. Yana da kyau mu sani, wannan lokacin NPower zai dauki masu karatu da marasa karatu, kowa zai iya nema.

8. (Employment and other details page) za'ayi maka wasu tambayoyi wanda zaka amsa su, daga karshe zaa bukaci ka Ɗora hoton ID card dinka; mu sani cewa katin ɗan ƙasa (National ID card) ko katin zaɓe (voters card) ko lasisim tuƙi (Drivers license) KO katin hawa jirgi (international passport) ne kaɗai zaka iya sakawa a wannan waje

9. Abin lura, N-teach da N-health za'a dauki wanda suke da Degree ne kawai, amma a bangaren N-health za'a fi bada ƙarfi da ɗalibai masu Diploma, HND da degree a bangaren medicine, physiotherapy, nursing, midwifery, da sauran kwasa-kwasai wanda suke da alaka da lafiya da kuma applied sciences).

GA wanda suke da Degree da HND zaa bukaci su saka hoton Shaidar gama NYSC da Shaidar Gama Makaranta (Degree Certificate)

10. Shawara ka duba abubuwanda da ka cike (review) kafin kayi submitting.

11. Bayan ka tura ka gama (submitting) zaa turo maka da wata lambar (Unique ID) ka kwafe ta ka ajiye ta kyan-kyan kada ka manta, kayi mata ajiyar kudi.

Muna muku fatan nasara. Yan Arewa ku dage ku shiga ku cike ku samu nasara.
 Ku yaÉ—a wannan yaje ko'ina.

Allah ya bada nasara

Sako daga Shafin
@Arewa Intellectual Youths Forum.
CEO http://admobiblog.com.ng

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel