Jami'an tsaro sun kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da surukin Buhari
Friday, May 10, 2019
Add Comment
Manyan wadanda ake zargi da yin garkuwa da surukin Shugaba Muhammadu Buhari, wato Magajin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, sun fada komar jami’an tsaro. Babban Hafsan rundunar sojin ruwan Najeriya, Riya Admiral Ibok Ekwe Ibas, shi ne ya bayyana hakan, jim kadan da kammala ganawa akan tsaro da shugaba Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja, a yau Alhamis.
Ibas, na Magana ne a madadin takwarorinsa, na mayakan kasa da kuma na sama, ya ce nan bada jimawa ba, za a cafke wadanda suka yi garkuwa da basaraken gargajiyar. Idan dai za a iya tunawa, an sace basaraken ne a ranar 1 ga watan Mayu, a gidansa, cikin garin Daura. Kuma kwanaki takwas bayan garkuwa da shi, har yanzu ba a sake jin duriyarsa ba. Yana auren diyar ‘yar uwan Buhari.

0 Response to "Jami'an tsaro sun kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da surukin Buhari"
Post a Comment