Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar mafi karancin albashi

Shugaba Muhammadu Buhari ya rabbata hannu kan dokar karin albashi mafi karanci na naira 30,000 a Najeriya. Hakan yana nufin daga wannan watan N30,000 shi ne albashi mafi karanci da ma'aikata za su karba a fadin Najeriya baki daya, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana a shafinta na Twitter ranar Alhamis. "Shugaba Buhari ya sanya wa sabuwar dokar mafi karancin albashi hannu. Daga yanzu N30,000 ne mafi karancin albashin," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa "dokar za ta fara aiki nan take kuma ta shafi kowane ma'aikaci." A ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta NLC ta bai wa Shugaba Buhari zuwa 1 ga watan Mayu a matsayin wa'adin ko dai ya saka hannu a kan dokar, ko kuma ta dauki mataki. Tun a shekarar 2015 ne Buhari ya yi alkawarin yi wa dokar kwaskwarima. Amma sai a Disambar 2017 shugaban ya kafa kwamitin da zai duba yiyuwar karin albashin bayan yajin aiki da NLC din ta gudanar a lokuta daban-daban. Jim kadan bayan gabatar da rahoton kwamitin gwamnonin jihohin kasar suka ce ba za su iya biyan N30,000 ba kamar yadda kwamitin ya bayar da shawara. Gwamnonin sun kekashe kasa cewa sai dai a rage ma'aikata indai ana so su biya N30,000 a matsayin albashi mafi karanci. A karshen watan Janairun 2019 Shugaba Buhari ya aike da gyaran kudirin dokar da zai ba shi damar aiwatar da karin albashin ga majalisar tarayya don neman amincewarta. N27,000 ne shugaban ya aike wa majalisar, inda ita kuma bayan muhawara ta kayyade 30,000 a matsayin mafi karancin albashin a ranar 19 ga watan Maris na shekarar 2019. A ranar Alhamis ne shugaban ya sanya wa dokar hannu, wadda za ta fara aiki nan take.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar mafi karancin albashi"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel