Barcelona Za Ta Yi Gwanjon ‘Yan Wasanta.
Friday, April 5, 2019
Add Comment
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta shirya yin zazzagar siyar da ‘yan wasanta a kokarin da kungiyar takeyi na tattara kudaden da zata sayi sababbin ‘yan wasa da su a kakar wasa mai zuwa bayan da tuni ta saka wasu daga cikin ‘yan wasanta a kasuwa. Kawo yanzu dai Barcelona ta bawa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid tazarar maki takwas a gasar laliga sannan kuma ta samu zuwa matakin kusa dana kusa dana karshe a gasar cin kofin zakarun turai sai dai kociyan kungiyar ya bayyana cewa yana son sake da yawa daga cikin ‘yan wasan da basa yiwa kungiyar amfani. Dan wasan da ake ganin zai fara barin kungiyar shine Philliph Coutinho wanda tun bayan komawarsa kungiyar baya abin arziki kuma kungiyar tana ganin idan ta siyar dashi zata samu makudan kudade. Har ila yau ana ganin kungiyar zata siyar da dan wasanta na baya dan kasar Faransa, Samuel wanda yake fama da ciwo a wannan kakar sai dan wasa Iban Rakitic wanda shima ake ganin zai iya barin kungiyar a kakar wasa mai zuwa. Sabon dan wasan kungiyar Malcom da mai tsaron raga Jasper Cillessen da dan wasan kasar Sipaniya Rafinha da takwaransa Danis Suares wanda kawo yanzu yake zaman aro a Barcelona suma suna cikin ‘yan wasan da zasu bar kungiyar a karshen wannan kakar. Tuni dai aka fara alakanta kungiyar da siyan dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antonio Griezman da kuma dan wasan tsakiyar Manchester United, Juan Mata wanda kwantaraginsa zai kare a kungiyar a karshen wannan kakar.
0 Response to "Barcelona Za Ta Yi Gwanjon ‘Yan Wasanta."
Post a Comment