A yayin da ya rage saura kwanaki kalilan a zaben cike gibi na gwamnan Kano, al'ummar mazabar Gama wacce kuri'unta ne za su raba gardama a zaben, sun wayi gari da ganin gwamnati na gudanar da ayyukan ci gaban kasa a yankin nasu. Mazauna gundumar ta Gama sun shaida wa BBC cewa sun kwashe shekara da shekaru suna fama da matsaloli da suka hada da karancin ruwa, da hanyoyi, da asibitoci, da ma sauran abubuwa da dama, ba tare da gwamnati ta kula su ba.
Wata mata da BBC ta zanta da ita ta ce sukan yi tafiya mai nisa, wadda ta hada har da shiga mota kafin zuwa inda za su samo ruwa na amfanin yau da kullum. Sai dai a yanzu haka gwamnati ta fara aikin gina fanfon burtsatse guda 11 a wannan yanki na gama domin shawo kan wannan matsala ta karancin ruwa. Baya ga fanfon burtsatse akwai kuma aikin hanya da aka fara a baya, wanda shi ma gwamnati take kammalawa, duk a gabanin zaben cike gibi na 23 ga watan Maris. Sai dai wasu al'umma a ciki da wajen gundumar na ganin cewa gwamnatin ta fara wadannan ayyuka ne domin neman kuri'a a zaben na ranar Asabar. Tuni dai aka samu rahotanni na sayen kuri'a a yankin, inda rundunar 'yan sanda a jihar ta bayar da sanarwar kame wasu da ake zargi da sayen katunan zabe a wurin al'umma. A hirarsa da BBC, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ayyukan da ake yi suna cikin wadanda gwamnati ta tsara tun fil-azal. A cewar sa 'wannan aiki dama yana kan layi, amma a wannan karo ne Allah Ya sa za a yi shi yanzu.'
A ranar 23 ga watan Maris ne hukumar INEC za ta sake yin zabe a wasu mazabu a Kano bayan sanar da cewa ba a kammala zaben jihar ba, wanda aka gudanar a ranar 9 ga Maris. Fafatawa a zaben da za a sake a Kano ta shafi 'yan takarar manyan jam'iyyu biyu ne, gwamna Ganduje na APC da kuma babban mai hamayya da shi Abba Kabir Yusuf na PDP. Sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris ya nuna jam'iyyar PDP mai hamayya ke gaba da yawan kuri'a 1,014,343, yayin da jam'iyyar APC wadda ke mulkin jihar ke da kuri'a 987,829. Zaben na ranar 23 ga watan Maris ne zai tantance wanda zai mulki jihar a shekara 4 masu zuwa.
CEO http://admobiblog.com.ng
0 Response to "Muna yin aiki tsakani da Allah ne a Gama - Dr. Abdullahi Ganduje."
Post a Comment