Sheikh Hasina ta sake zama firai ministar Bangladesh a karo na biyu.

Tun shekarar 2009 ta ke rike da madafin iko a Bangladesh. Jam'iyyun adawa sun yi tir da abin da suka kira "zaben bogi", wanda aka sami tashin hankali da korafe-korafe na magudin zabe. Jam'iyyar adawar ta sami kujeru bakwai ne kawai, kuma ta yi kira da a sake gudanar da wani zabe. "Muna kira ga hukumar zabe da ta soke wannan zaben bogin nan take," inji Kamal Hossain wanda shi ne jagoran jam'iyyar adawa. Ya kuma kara da cewa "Muna bukatar a sake gudanar da wannan zaben a karkashin wata gwamnatin rikon kwarya nan ba da jimawa ba". Hukumar Zabe ta Bangladesh ta gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ta sami rahotanni "daga sassan kasar daban-daban" da ke cewa an tafka magudi, kuma ta ce za ta bincike lamarin. Akalla mutum 17 sun rasa rayukansu a hargitsin da ya biyo bayan zaben tsakanin magoya bayan jam'iyya mai mulkin kasar da masu goyon bayan jam'iyyar adawa. 'Yan takara 47 sun janye daga tsayawa takara daf da a kammala kada kuri'a, bayan da suka yi zarhin an tafka magudi. Ms Hasina ta fada wa BBC ranar Juma'a cewa "A bangare daya suna yin korafi. A daya bangaren kuma, suna sukar ma'aikatan jam'iyyarmu da shugabanninta. Wannan ne abin takaici da ke damun kasarmu".
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Sheikh Hasina ta sake zama firai ministar Bangladesh a karo na biyu."

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel