Mutane sama da 22,000 ne suka kamu da cutar korona virus a Nijeriya.
Wednesday, June 24, 2020
Mutane kusan 650 ne aka ba da rahoton sun sake kamuwa da cutar korona a ranar Laraba. Yanzu yawan masu cutar a Najeriya 22,020 ne.
A baya-bayan nan dai Najeriya na fitar da ɗaruruwan alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar, wadda ta fara ɓullar a ƙasar ƙarshen watan Fabrairu.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta nuna cikin alƙaluman da ta fitar a daren Laraba cewa har yanzu Lagos, ita ce ke kan gaba a yawan mutanen da aka sake ganowa sun kamu, da 250.
Adadin masu korona a Lagos dai ya Kai 10,000. A jihar Oyo cutar ta sake kama mutum 100.
Yayin da bayanan ke nuna cewa annobar ta kashe mutum tara a Najeriya ranar Laraba.
Jihohin Filato da Delta kuma, an tabbatar mutum 40 ne suka kamu da cutar baya-bayan nan cikin kowaccensu. Sai mutum 28 a jihar Abia.
Haka kuma, an sake gano sabbin masu korona 27 a jihar Kaduna ranar Laraba. Sai Ogun, mai mutum 22.
A Edo, korona ta sake harbin mutum 20, yayin da aka gano mutum 18 ranar Larabar a jihar Akwa Ibom.
An kuma ba da rahoton mutum 17 sun sake kamuwa a jihar Kwara, da kuma makamancin wannan adadi a Abuja.
Karanta>> Sharuda takwas da kasar Saudiya ta gindaya domin gudanar da aikin Hajjin bana
Sai Enugu, mai mutum 14, Neja da Adamawa, an gano ƙarin mutum 13 da suka kamu da korona a cikin kowaccensu.
Ƙarin jihohin da aka samu masu korona ranar Laraba, akwai Bayelsa mai mutum 7. Sai Osun da Bauchi, mutum 6
Anambra, mutum 4, sai Gombe 3, jihar Sokoto an sake gano masu korona 2.
Jihohin Imo da Kano, mutum 1 a cewar alƙaluman hukumar NCDC. BBC