Kungiyar kasashen turai ta tara euro bilyan 7 domin samar da maganin rigakafin covid -19
Saturday, June 27, 2020
Taurarin 'Yan wasa, masu shirin fina finai da masu tallata kayan kawa sun taimakawa kungiyar kasashen Turai wajen tara kudin da ya kai kusan Dala biliyan 7 a ranar asabar, a karkashin Gidauniyar da Hukumar Gudanarwar Turai ta kaddamar domin tara kudin da za'a samar da maganin rigakafin cutar coronavirus da za'a baiwa kasashe matalauta.
Shugabar gudanarwar kungiyar Turai Ursula von der Leyen ta kaddamar da gidauniyar inda ta sanar da bada kusan euro biliyan 5 daga Bankin zuba jarin Turai da kuma kungiyar, yayin da gwamnatoci da attajirai suka yi alkawarin bada euro biliyan 10 abinda ya kawo adadin kudin da aka samu tun bayan kaddamar da gidauniyar ranar 4 ga watan Mayu zuwa euro miliyan 15 da miliyan 900.
Von der leyen tace za'a magance wannan annoba ne kawai idan an shawo kanta a kowanne sako na duniya.
Karanta>>> Sanarwa: Manhajar Abu Hanifa Tv Ta Fito
Karanta>>> Sanarwa: Manhajar Abu Hanifa Tv Ta Fito
Cikin taurarin da suka taka rawa wajen kaddamar da gidauniyar sun hada da Coldplay da Milley Cyrus da Jennifer Hudson da Dwayne 'The Rock', yayin da attajiri Bill da Melinda Gates da shugaban hukumar lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus suka halarci bikin.
Kungiyar kasashen Turai tace gwamnatocin kasashe 40 suka shiga shirin, kuma akasari sun bada gudumawar su ga Hukumar Lafiya da Hukumar Samar da abinci. rfi