Daliban Gidauniyar Kwankwasiyya sun sauka a kasar Indiya.
Thursday, September 26, 2019
Add Comment
Dalibai 105 daga cikin 242 da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin karatunsu sun sauka a kasar Indiya.
Daliban dai sun sauka a filin tashi da saukar Jirage na Indira Gandhi dake birnin New Delhi, babban birnin kasar.
A jiya Talata dai akayi bankwana da daliban a jihar Kano, inda daga nan ne suka tafi jihar Legas, a nan ne suka hau jirgi zuwa hadaddiyar daular Larabawa kafin daga bisani suka sauka a kasar ta Indiya.
Mafiya daliban da suka tafi a ranar Talata, daliban Jami'ar Mewar ne dake jihar Rajasthan a Arewacin India.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Kwankwaso ya bayyana cewa; "Jirgin karshe na daliban zai tashi ne ranar Laraba, 2 ga watan Oktobar 2019.
0 Response to "Daliban Gidauniyar Kwankwasiyya sun sauka a kasar Indiya."
Post a Comment