Gwamnatin Tarayya za ta raba ma gwamnatocin jihohi naira biliyan 649.434 ragowar kudin Paris Club.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kwanan nan za ta raba ma gwamnatocin jihohi naira biliyan 649.434 ragowar kudin Paris Club da yayi saura. Ministar kudi, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a ja ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu, lokacin da ta ke jawabi ga manema labarai, a taron ‘yan jaridu da ta shirya. Wannan adadi dai bai kai ma naira bilyan 694.560 da Babban Bankin Najeriya (CBN ) ya biya cikin watan Maris, 2019 ba. Aan tattaro cewa bambancin canjin musayar kudade ne ya kawo wannan gibi na sama da naira milyan 40.
Ministaar ta ce nan ba da jimawa ba za a fara raba wa jihohi kudaden, a matsayin kashin karshe na kudaden Paris Club da aka sha ba su a baya. Ragowar kudin Paris Club: Za a yi wa jihohi rabon N649bn Zainab ta ce wannan tsari na bai wa jihohi kudaden Paris Club, ya samu nasara gagarima wajen cicciba kasar nan ta fita daga matsin tattalin arziki da ta yi fama da shi. An gudanar da tsarin ne a karkashin Shirin Farfado da Tattalin Arziki a karkashin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Zainab ta kara da cewa sakamakon nasarar wannan shiri, a yanzu Najeriya na kan hanyar dorewa a kan ingantaccen tattalin arziki.
CEO http://admobiblog.com.ng

0 Response to "Gwamnatin Tarayya za ta raba ma gwamnatocin jihohi naira biliyan 649.434 ragowar kudin Paris Club."

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel