Jami'an tsaro sun cafke ‘Yan Luwadi 3 a Jihar Katsina.
Wednesday, March 6, 2019
Add Comment
Jami'an rundunar yan sandan Nijeriya na Katsina ta sanar da nasarar cafke wani mutum mai suna Aminu Mai Unguwa Tsanni, mai shekaru 45 da haihuwa bisa laifin yin luwadi da wasu mutane biyu ba tare da ya biya su kudin da suka shirya ba, a wani hotel din Katsina.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isa ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da manema labarai suka fitar a jihar ta Katsina wanda ya nuna tuhumar wani Aminu Mai Unguwa Tsanni, da laifin yin luwadi da Abdullahi Abubakar, mai shekaru 20 da kuma Rabi'u Yahuza, mai shekaru 23 dukkan su a garin Katsina.
An sami nasarar damke mutanen ne bayan wanda ake zargin yin luwadi da su, ya gaza biyan su kudin alkawarin da ya yi masu na naira dubu goma-goma kowannensu, amma da ya gama biyan bukatarsa dasu sai ya gudu ba tare da ya basu ko sisin kwabo ba, inda su kuma suka yi awon gaba da wayoyin hannunsa har guda biyu.
Wannan ne ya harzuka Mai Unguwa Tsanni, inda ya yi karar mutanen biyu a ofishin yan sanda dake Sabon Gari cikin birnin Katsina, bisa zarginsu da sace masa wayoyin hannunsa.
Da binciken yan sanda ya tsananta ne aka gano cewa akwai lauje cikin nadi game da satar da aka yi masa, akwai alamun cewa lalata ya yi da su bai biya su ba.
Tuni yan sandan suka maka su a gaban kuliya manta sabo domin cigaba da gano yadda ba'asin ya kasance, domin yi masu hukuncin da ya dace.
0 Response to "Jami'an tsaro sun cafke ‘Yan Luwadi 3 a Jihar Katsina."
Post a Comment