Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga Atiku Abubakar
Monday, January 21, 2019
Add Comment
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya gana da tsohon mai gidansa Cif Olusegun Obasanjo kuma sun ci abincin rana tare a garin Abeokuta na jihar Ogun.
Ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, kuma ya wallafa hotunansa tare da Obasanjo da malamin addinin Musulunci Dr Ahmad Gumi da malamin addinin Kirista Bishop Mathew Hassan Kuka wadanda ake zaton tare aka yi ganawar da su.
Olusegun Obasanjo dai na daya daga cikin masu fada a ji a fagen siyasar Najeriya.
Kuma ya nuna goyon bayansa ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya lashe zaben 2015, sai dai a bana ya ce ba ya goyon bayan shugaban ya nemi wa'adi na biyu a zaben shekarar 2019.

0 Response to "Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga Atiku Abubakar"
Post a Comment