Rundunar 'yan sanda ta damke wadanda suka sace 'yan biyun jihar Zamfara.
Monday, December 31, 2018
Add Comment
Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun damke wasu yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya. Wadannan yan ta'addan ne suka sace wasu yan mata yan biyu kwanakin baya. Babban jami'in hukumar yan sanda, DCP Abba Kyari ya bayyana hakan ne a ranan Litinin, 31 ga watan Disamba, 2018 a shafinsa ta Facebook inda ya jero sunayensu: 1) Nafiu Usman 28yrs a.k.a Baba Doctor, 2) Ma'aruf Usman daga Wanari a Zurmi 3) Inusa Usman 40yrs daga Zurmi 4) Awal Jibril 41yrs daga Mada LGA 5) Shehu Mohammed 55yrs 6) Alhaji Ibrahim Ibrahim 35yrs 7) Ibrahim Sani 45yrs 8) Kabiru Usman 30yrs 9) Bala Garba 60yrs 10) Maigari Labbo 56yrs 11) Mohammed Abdullahi Aramako 31yrs 12) Salisu Mamman Wadatau 38yrs daga Danjibga Idan za’a tuna a ranar 25 ga watan Oktoba ne aka samu rahoton sace yan matan da wata gungun masu garkuwa da mutane suka yi a lokacin da suke kan hanyar raba ma yan uwansu da kawayensu ankon bikinsu wanda ake gab da gudanar da bikin. An sace yan matan ne a karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Abubakar Muhammad ya bayyana, inda yace an sace mutane bakwai a cikin kwanaki biyu, daga cikinsu har da tagwayen. Daga baya suka bayyana cewa zasu kashe tagwayen matukar ba’a biya musu bukatarsu na biyan kudin fansa ba. Ba da dadewa ba aka sako yan matan bayan gudunmuwar da wasu yan siyasan jihar suka taimaka da kudin fansar naira miliyan 15.
0 Response to "Rundunar 'yan sanda ta damke wadanda suka sace 'yan biyun jihar Zamfara."
Post a Comment